Connect with us

News

Majalisar Dokokin Kano Na Shirin Gyara Dokar Da Ta Kafa Kotunan Shari’ar Musulunci

Published

on

Majalisar Dokokin Kano Ta Ce Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Zaben Kananan Hukumomin Da Aka Shirya Yi

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara aiki kan kudurin gyara dokar da ta kafa kotunan shari’ar Musulunci da kuma kotunan daukaka kara na addinin Musulunci, domin magance sarkakiyar da ake samu tsakanin hukuncen wadannan kotuna da na kotunan majistare.

An gabatar da kudurin ne ta hannun mataimakin kakakin majalisar, kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Rimin Gado, Muhammad Bello Butu-Butu, wanda ya ce lokaci ya yi da za a sabunta dokar domin dacewa da tsarin shari’a na zamani.

Advertisement

Himma Radio 91.1FM Ta Dauki Nauyin Sanya Yara A Makaranta A Kano

A cewarsa, tun bayan kafa kotunan shari’ar Musulunci a jihar Kano a shekarar 2000, akwai wasu sassa da ba su samu cikakken tanadi a dokar ba, abin da ke haifar da ruɗani a wajen aiwatar da shari’o’i.

“Dole ne mu gyara dokar domin mu fayyace hurumin kotunan Musulunci da na majistare, domin kada a rika samun rikici ko rashin fahimta tsakanin su,” in ji Butu-Butu.

Advertisement

Ya kara da cewa dokar da ke tafiyar da kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci ta kai kusan shekaru 50 da samar da ita, don haka akwai bukatar sabunta ta domin ta dace da tsarin rayuwar yau da kullum.

A cewar rahoton wakilin Premier Rediyo a Kano, Kamal Umar Kurna, majalisar ta kuma bayyana cewa daga cikin gyaran da za ta yi, za ta bai wa bangaren sulhu muhimmanci, domin rage cinkoson da ake samu a kotuna da kuma jinkiri wajen yanke hukunci.

Advertisement

Majalisar ta ce yin hakan zai taimaka wajen ganin cewa wasu matsalolin ana warware su cikin lumana ta hanyar sasantawa, maimakon kai su kotu kai tsaye.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending