News
Iran Ta Ce Za Ta Yi Hulda Da Amurka Ne Kawai Idan Ta Daina Goyon Bayan Isra’ila
Jagoran addinin Islma a Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya ce Tehran za ta yi la’akari da yin hulda da Amurka ne kawai idan ta daina goyon bayan Isra’ila, kana kuma ta janye dakarunta daga yankin Gabas ta Tsakiya, da daina tsoma baki a al’amuran yankin.
Khamenei ya fadi haka ne yayin taron dalibai a bikin cika shekaru 46 da mamaye ofishin jakadancin Amurka, a 1979 a Tehran babban birnin kasar.
Kalaman jagoran na zuwa ne bayan yakin kwanaki 12 ya barke a watan Yuni, sakamakon hare-haren Isra’ila ta kai kamn kan Iran, lamarin da ya jawo Washington ta shiga kai farmaki kan wuraren nukiliyar Iran. Rikicin ya dakatar da tattaunawar nukiliya da aka jima ana yi tsakanin Iran da Amurka.
Tun bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya a watan Yuni, Iran na cigaba da fama da takunkuman karayar tattalin arziki daga kasashen yammacin duniya, musamman tun bayan janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya a 2018. Majalisar Dinkin Duniya ta sake farfado da wasu takunkumin a watan Satumba, bayan Birtaniya da Faransa da Jamus suka safe farfado da tsarin.
A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce a shirye su ke su koma teburin tattaunawa da Washington amma kan batun Nukiliya kawai, babu batun da ya shafi mizanin makami mai linzami.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News16 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
