Connect with us

News

‎Wasu Ɓata-gari Sun Yashe Ofishin Shugaban Ƙaramar Hukuma A Kano  ‎

Published

on

kaduna kano

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, wasu ɓarayi da ba a tantance ko su waye ba sun fasa ofishin Shugaban Ƙaramar Hukumar Gaya, Alhaji Mahmoud Tajo Sani, inda suka sace kayayyakin da ofishin ke amfani da su, ciki har da na’urorin hasken rana (solar).

‎Lamarin ya faru ne a daren Talata, kamar yadda mai ba wa shugaban shawara kan yaɗa labarai, Kwamared Naziru Mukhtar Gaya, ya tabbatar a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Advertisement

Majalisar Tarayya Ta Amince Da Daurin Shekara 14 Ga Malamai Masu Lalata Da Ɗalibai

‎A cewarsa, fashin ya jefa al’umma da mahukunta cikin damuwa, inda ya bayyana shi a matsayin abin kunya da takaici.

‎“Wasu ɓata-gari sun kutsa cikin ofishin shugaban ƙaramar hukuma a daren Talata, suka sace muhimman kayayyakin da ake amfani da su wajen gudanar da aiki,” in ji Kwamared Naziru.

Advertisement

‎Sai dai ya bayyana cewa ba a tantance jimillar darajar kayan da aka sace ba, amma ya ce jami’an tsaro sun fara bincike domin damƙo waɗanda ke da hannu a lamarin.

‎Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayanin bincikensu ba, amma an ce ana ci gaba da aikin ganowa da bin diddigin ɓarayin.

Advertisement

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending