Connect with us

News

Ɗalibai Sun Yi Ajalin Malaminsu Sakamakon Dukan Kawo Wuka Da Suka Yi Masa

Published

on

Unguwa gawa

Wani malami a makarantar Soun High School, Mista Fatai Adegoke, ya mutu bayan da dalibansa suka far masa da duka har suka yi masa muggan raunuka.

‎Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan da malamin ya kama wasu dalibai suna caca a lokacin karatu, inda ya yi musu tsawatarwa tare da kokarin hana su.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Kuɓutar Da Mutum 86 Da Boko Haram Suka Yi Garkuwa Da Su

‎Sai dai daliban cikin fusata suka yi masa kwanton bauna, suka daki malamin da duka mai muni, lamarin da ya kai ga karya masa kafafu biyu da kuma jikkata shi matuka.

‎An garzaya da shi asibiti domin samun kulawa, amma daga baya likitoci sun tabbatar da rasuwarsa sakamakon tsananin raunukan da ya samu.

Advertisement

‎A cikin sakon ta’aziyya, kungiyar malamai ta ce lamarin ya girgiza su matuka.

‎ “Mun kadu da alhinin wannan danyen aiki. Wannan hari ba a kan malami kadai ba ne, hari ne ga mutuncin ilimi baki daya,” in ji sanarwar kungiyar.

Advertisement

‎Kungiyar ta yi kira ga Kungiyar Malaman Najeriya (NUT), hukumar TESCOM, da jami’an tsaro da su tabbatar an cafke wadanda suka aikata laifin tare da hukunta su.

‎Majiyoyi sun bayyana cewa daliban da ake zargi sun tsere bayan aikata laifin, lamarin da ya jawo zanga-zangar damuwa da fushi a tsakanin mazauna yankin.

Advertisement

‎Yayin da Daily South Nigeria ta yi kokarin samun karin bayani daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, wayarsa ba ta shiga ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending