Connect with us

News

Aƙalla Matasa 12 Ne Suka Mutu A Turmutsutsun Neman Aikin Soja A Ghana

Published

on

stampede ghana army recruitment event kills 6 wounds 22 1762961485 9804

Aƙalla mutum 12 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani turmutsutsu da ya faru yayin jarabawar ɗaukar aikin soja a Filin Wasa na El-Wak da ke Accra, babban birnin ƙasar Ghana.

Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da ɗaruruwan matasa masu neman aikin suka kutsa cikin filin wasan ba tare da bin tsarin shiga da aka tanada ba.

Advertisement

An Gano Motar Da A Ka Sace A Gidan Gwamnatin Kano

Rundunar Tsaron Ghana (GAF) ta ce mutum shida ne suka mutu a farko, amma rahotanni daga asibitin sojoji sun tabbatar da cewar adadin mamatan ya ƙaru zuwa mutum 12.

Wasu mutum 22 sun jikkata, ciki har da biyar da ke cikin mawuyacin hali, kamar yadda jami’ar asibitin sojojin ƙasar ta tabbatar.

Advertisement

Ministan Tsaro, Dokta Cassiel Ato Forson, ya ce an dakatar da ɗaukar na wani ɗan lokaci tare da kafa kwamiti domin binciken musabbabin lamarin, wanda ta bayyana a matsayin abin takaici.

Shugaban ƙasar, John Mahama, ya kai ziyarar jaje ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma marasa lafiya, inda ya bayyana cewa gwamnati za ta ɗauki matakan tabbatar da cewa irin wannan lamari ba zai sake faruwa ba.

Advertisement

Rundunar Tsaron Ghana ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da kula da waɗanda suka jikkata a asibitin sojoji.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending