News
An Kama Mutum 3 Kan Zargin Safarar Yara 17 A Zariya
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da hannu a safarar yara, inda aka ceto yara 17 da ake zaton an shirya tura su Abuja da wasu sassan ƙasar har ma da ƙetare.
A cewar wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, an kama mutanen ne da misalin ƙarfe 4 na yammacin Laraba a ƙarkashin gadar Ɗan Magaji da ke unguwar Wusasa, bayan samun sahihin bayanin sirri.
Wasu Batagari Sun Kashe Uwargida Da Amarya, Sun Banka Wa Gawarsu Wuta A Kano
Ya bayyana cewa jami’an sashen Ɗan Magaji sun yi gaggawar kai samame, inda suka tarar da yara ƙanana 17 tare da waɗanda ake zargin suka tattaro su daga jihohi daban-daban da nufin kai su Abuja.
DSP Hassan ya ce waɗanda ake zargin sun haɗa da:
Musa Shu’aibu, mai shekara 21, daga Funtua, Katsina, Sani Mamman, mai shekara 23, daga Ingawa, Katsina, Mubarak Isma’il, mai shekara 20, daga Unguwa Uku, Kano.
A cewar kakakin rundunar, waɗanda ake zargin sun amsa cewa su ne suka tattaro yaran daga wurare daban-daban da zummar kai su babban birnin tarayya, kafin jami’an tsaro su tarwatsa shirin.
Rundunar ta tabbatar da cewa yaran suna cikin ƙoshin lafiya, kuma a halin yanzu suna hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano iyayensu ko masu kulawa da su.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yaba da bajintar jami’an da suka gudanar da samamen, tare da nanata cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in safarar yara ko cin zarafinsu ba
