News
Wasu Batagari Sun Kashe Uwargida Da Amarya, Sun Banka Wa Gawarsu Wuta A Kano
A Jihar Kano, wasu mutane da ba a gano ko su wane ba sun kashe wata Uwargida da Amarya, sannan suka banka wa gawar ɗaya daga cikinsu wuta, a wani mummunan hari da ya faru a unguwar Tudun Yola da ke ƙaramar hukumar Gwale kamar yanda Arewa Rediyo ta ruwaito.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a jiya a cikin gidan Alhaji Ashiru Shu’aibu , inda maharan suka kutsa cikin dare suka hallaka matan nasa biyu ba tare da tausayawa ba.
Alhaji Ashiru ya ce batagarin sun shiga gidan ne cikin tsakar dare, inda suka yi wa matansa kisan gilla, kafin daga bisani su ƙona gawar ɗaya daga cikinsu.
A cewarsa, “Sun shigo gidanmu cikin dare, suka kashe matana, sannan suka ƙona gawarsu. Har yanzu ban san dalilin wannan aika-aika ba.”
Rahotanni sun ce faruwar lamarin ta tayar da hankalin mazauna yankin, inda mutane ke nuna damuwa kan yadda ake samun irin waɗannan hare-hare a cikin unguwannin Kano.
Rundunar ‘yan sandan Kano har yanzu ba ta fitar da sanarwa ba dangane da faruwar lamarin,
-
News6 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
