Connect with us

News

DSS Ta Sake Kama Ɗan Ta’addan Ansaru Da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje

Published

on

DSS (1)

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta sake kama Abdulazeez Obadaki, wani babban memba na ƙungiyar Ansaru da ya tsere daga gidan gyaran hali na Kuje lokacin da aka afka wa kurkukun a 2022.

A cewar DSS, an kama Obadaki ne bayan wasu samame da jami’an tsaro suka gudanar a wurare daban-daban, inda ake zargin ya shafe lokaci mai tsawo yana ɓoye.

Advertisement

NSCDC Ta Karrama Ma’aikacin Wucin Gadi da Ya Mayar Da  Naira Miliyan 20 Da Ya Tsinta A Kano

Obadaki na ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da kai harin Makarantar Cocin Deeper Life a Okene, Jihar Kogi, a 2012 — wani hari da ya tayar da hankalin jama’a a lokacin.

Hukumar ta kuma ce ana zargin shi da hannu a wasu manyan laifuka, ciki har da harin bankuna a Uromi, Jihar Edo, da wasu ayyukan ta’addanci da suka shafi jihohin arewacin Najeriya.

Advertisement

DSS ta bayyana cafke shi a matsayin wata “babbar nasara” da za ta taimaka wajen murkushe ragowar ƙungiyar Ansaru da inganta tsaro a ƙasar.

 

Advertisement

Channels TV 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending