Connect with us

News

Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya Ta JOHESU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Najeriya

Published

on

JOHESU Strike

Haɗakar JOHESU da ke ƙunshe da ƙungiyoyin ma’aikatan ɓangaren lafiya ta sanar da tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Asabar 15 ga watan Nuwamban 2025 bisa iƙirarin da ta yi na cewa gwamnatin Najeriya ta gaza aiwatar da gyare-gyare a tsarin biyan albashin mambobinta tsawon shekaru 12.

Yajin aikin na JOHESU na zuwa dai dai lokacin da yajin aikin ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriyar NARD ke cika kwanaki 15 da farowa ba tare da alamun juya baya ba, ko kuma sasantawa tsakaninsu da gwamnatin ƙasar ba.

Advertisement

DSS Ta Sake Kama Ɗan Ta’addan Ansaru Da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje

A cewar JOHESU tsawon lokaci gwamnatin Najeriya ta ƙi mayar da hankali wajen aiwatar da gyaran da aka yiwa albashin ma’aikatan ɓangaren lafiyar ƙarƙashin CONHESS, haka zalika gwamnatin ta gaza warware matsalar alawus-alawus dama yanayin walwala da jin daɗin ma’aikatan tsawon shekaru.

Sanarwar fara yajin aikin da JOHESU ta fitar a daren jiya Juma’a aka kuma raba ga manema labarai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Comrade Kabiru Ado Minjibir ta bayyana cewa ya zame musu wajibi tsunduma yajin aikin a halin yanzu.

Advertisement

Wannan yajin aiki na JOHESU na zuwa a dai dai lokacin da Najeriya ke fama da raɗaɗin yajin aikin ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa NARD waɗanda suka tafi yajin aikin tun a farkon watan nan sakamakon rashin biyansu wasu alawus-alawus da gurguncewar yanayin aikinsu dama rashin walwala wanda suma tsawon lokaci suka cimma jituwa da gwamnati amma aka gaza aiwatarwa.

Wannan yajin aikin ɓangarorin a lokaci guda waɗanda suke riƙe da asibitoci Najeriyar kai tsaye zai sake jefa kulawar lafiya a wani yanayi lura da yadda ya shafi kusan dukkanin asibitoci a dukkanin matakan ƙasar face masu zaman kansu da kuma na koyarwa wanda ƙwararrun likitoci zasu bayar da kulawa.

Advertisement

Haɗakar ta JOHESU dai na wakiltar tarin ƙungiyoyin ma’aikatan ɓangaren lafiya a Najeriya wanda rashinsu zai sake taɓarɓara ayyuka har a jami’o’i da kwalejojin kimiyya.

 

Advertisement

 

FRI HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending