News
’Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Jami’an Sa Kai 16 Tare Da Yin Garkuwa Da Mutane 42 A Neja
Akalla jami’an sa-kai 16 ne suka rasa rayukansu, yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutum 42 a hare-haren da suka faru a ƙauyuka daban-daban na ƙaramar hukumar Mashegu dake jihar Neja tsakanin Lahadi 9 zuwa Alhamis 13 ga Nuwamba, 2025.
Mazauna yankin sun ce hare-haren sun haifar da tsananin fargaba, lamarin da ya sa dubban mazauna yin kaura daga gidajensu domin tsira da rayuka.
Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya Ta JOHESU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Najeriya
Wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun fara kai hari ne a Dutsen Magaji a ranar Lahadi, inda suka sace mutum 22.
Ya ce, “Sa-kai sun bi su suka yi artabu da su. A wannan musayar wuta ne sa-kai uku suka mutu, mutane biyar kuma suna jinya.”
Sai dai, a cewar sa, ’yan bindigar sun dawo da sanyin safiya a ranar Alhamis, suka shiga ƙauyen Magama lokacin da jama’a ke cikin sallar asuba.
“Sun zagaye masallaci suka tafi da mutum fiye da 20. Wasu sa-kai sun bi sahunsu ba tare da sanin an yi musu kwanton bauna ba. ‘Yan bindigar suka bude wuta, inda sa-kai 13 suka rasa rayukansu,” in ji shi.
Mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Mashegu, Isah Ibrahim Bokuta, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce jami’an sa-kai da suka mutu sun nuna jarumta wajen kare al’ummarsu, inda ƙaramar hukumar ta bayyana godiya kan jajircewarsu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce za su binciki rahoton kafin su fitar da cikakken bayani.
A yanzu haka, mazauna da dama daga ƙauyuka kamar Dutsen Magaji, Borin-Aiki, Gidan Ruwa da Magama sun bar gidajensu, inda ake ce musu suna neman mafaka a Mashegu, Kawo-Mashegu, Manigi da wasu yankuna.
A wani lamari daban, tsohon shugaban SUBEB na jihar Neja, Alhaji Alhassan Bawa Niworo, har yanzu yana hannun masu garkuwa, duk da labarin cewa iyalansa sun biya naira miliyan 70 a matsayin kudin fansa.
An sace Niworo tare da wasu jami’an gwamnati a ranar 29 ga Satumba, 2025, a kan hanyar Mokwa–New Bussa da ke ƙaramar hukumar Borgu.
