Connect with us

News

Gidauniya ta Nemi Haɗin Gwiwa da Ma’aikatar Jin Ƙai don Shirye-Shiryen Ciyawar Ramadan

Published

on

IMG 20260124 WA0006

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gidauniyar Save Yateem Orphans ta bayyana aniyarta ta yin haɗin gwiwa da Ma’aikatar Jin Ƙai da Rage Talauci wajen gudanar da shirin ciyar da abinci a lokacin Ramadan mai zuwa.

Advertisement

Daraktar Gudanarwa ta gidauniyar, Hauwa’u Muhammad Hadi, ta bayyana haka ne a lokacin da take ganawa da Kwamishinan Ma’aikatar a ofishinsa.

Muslim Charity Organisation za ta Haɗa Gwiwa da Ma’aikatar Jin Ƙai don Tallafa wa Mabuƙata

Advertisement

Ta ce ziyarar tana da manufar haɗin gwiwa tsakanin gidauniyar da gwamnatin jihar ta ƙarƙashin ma’aikatar wajen ciyar da abinci a Ramadan, wanda aka keɓance ga marayu, zawarawa, almajirai, masu buƙatu na musamman da marasa galihu a faɗin jihar.

Hauwa’u ta bayyana cewa gidauniyar ta jin ƙai ce, ba mai neman riba ba, wadda aka samar domin tallafa wa walwalar marayu, kare martaba da haɓaka ci gabansu, wadda a tsawon shekaru ta kasance mai jajircewa wajen aiwatar da ayyukan da suka mayar da hankali kan al’umma domin rage wahala da dawo da fata mai kyau ga masu rauni.

Advertisement

Ta bayyana cewa yayin da ake shirin gudanar da ciyarwar Ramadan ta shekarar 2026, manufofin gidauniyar sun haɗa da faɗaɗa yawan masu cin moriyar shirin, tabbatar da daidaitaccen tsarin gudanarwa, kare martabar masu amfana da shirin da ƙarfafa tsarin ɗaukar nauyi, tana mai nuna damuwa da yadda wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke samun tallafi daga ƙasashen waje ke gudanar da shirin ba tare da cikakken tsari ba.

Ta bayar da shawarar cewa gwamnati, ta ƙarƙashin ma’aikatar, da ta ƙarfafa shirye-shiryen ciyarwar Ramadan, inda ta ce ƙungiyar tasu za ta bayar da gudummawa wajen tabbatar da cewa ƙungiyoyin suna bin ƙa’idojin jin ƙai da kare lafiyar masu cin moriyar shirin.

Advertisement

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Jin Ƙai da Rage Talauci, Aliyu Adamu Kibiya, ya gode wa gidauniyar bisa ziyarar da ta kawo da kuma nuna ƙwazo wajen tallafa wa walwalar al’umma.

Ya bayyana cewa ma’aikatar na maraba da duk wani mai bayar da tallafi da ke da niyyar taimaka wa gwamnati wajen rage wahalar da al’umma ke fuskanta, musamman masu rauni, a kowane lokaci.

Advertisement

Kwamishinan ya ƙara da cewa tun lokacin da gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta fara aiki, kowace shekara ana ware kuɗaɗe masu yawa don ciyarwar Ramadan don rage wahalar da al’umma ke fuskanta, inda dubban mutane ke cin moriyar shirin.

Ya tabbatar wa ƙungiyar cewa ma’aikatar za ta ci gaba da yin haɗin gwiwa da su da sauran ƙungiyoyin jin ƙai domin tabbatar da nasarar aiwatar da irin waɗannan ayyuka.

Advertisement

Daga ƙarshe, ƙungiyar ta ba kwamishinan lambar girmamawa saboda hidimarsa ta mai yawa wajen jin ƙai da walwalar al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending