Connect with us

News

Muslim Charity Organisation za ta Haɗa Gwiwa da Ma’aikatar Jin Ƙai don Tallafa wa Mabuƙata

Published

on

IMG 20260124 WA0007

Kwamishinan Ma’aikatar Jin Кai da Rage Talauci, Aliyu Adamu Kibiya, ya bayyana aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin bayar da tallafi domin inganta rayuwar marasa galihu.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar wata tawaga daga Muslim Charity Organisation wadda ta kai masa ziyara a ofishinsa.

Advertisement

Gwannan Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP.

Za a iya tunawa cewa ƙungiyar, wadda ke da shelkwata a ƙasar Ingila, a kwanan nan ta bayar da gudummawar mota bas mai kujeru 32 ga ma’aikatar domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan jin ƙai. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya karɓi gudummawar a madadin ma’aikatar.

Advertisement

Kibiya ya bayyana cewa daga cikin manyan ayyukan da aka ɗora wa ma’aikatar akwai samar da ayyukan jin ƙai ga al’ummar jihar, musamman marasa galihu, domin tallafa musu a fannoni daban-daban na rayuwa.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar na maraba da ƙungiyoyin jin ƙai da ke son taimaka wa gwamnati wajen tallafa wa jama’a ta hanyar koyar da sana’o’i, bayar da horon sana’o’i da sauran shirye-shiryen tallafi, yana mai gode wa ƙungiyar bisa gudummawar motar da ta bayar, ya ce hakan zai taimaka matuƙa wajen aiwatar da ayyukan jin ƙai a faɗin jihar.

Advertisement

Kwamishinan ya nemi ƙungiyar ta taimaka wa ma’aikatar wajen aiwatar da wasu ayyuka da suka haɗa da bayar da tallafi, tattara bayanai ta hanyar fasahar zamani, tallafa wa almajirai da samar da kayan makaranta da jakunkuna ga yara ɗalibai, ya ce kowane daga cikin waɗannan ayyuka yana da manufar inganta rayuwar al’umma da jin daɗin mabuƙata.

Tun da farko, Daraktan Shirye-shirye na ƙungiyar, Irfan Rajput, ya ce sun kai ziyarar ne domin ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu da ma’aikatar tare da tsara hanyoyin ci gaba da aiki tare domin inganta rayuwar marasa galihu.

Advertisement

Rajput ya ce za su kalli waɗannan buƙatu da ma’aikatar ta nema don ganin hanyar da za su shigo su taimaka, har ma da kawo ayyukan jin ƙai masu yawa jihar Kano.

Ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ma’aikatar domin tabbatar da nasarar aiwatar da waɗannan ayyuka a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending