Connect with us

Politics

Zaɓen 2027: Matashin dan jarida Ya amsa kiran al’ uammar Akko ta Arewa

Published

on

IMG 20260130 WA0009
Spread the love

Dan jarida Usman Abubakar Usmaniyya, ya sanar da a niyyarsa ta tsayawa takarar ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe a zaɓen shekarar 2027, bayan abin da ya bayyana a matsayin kiraye-kirayen da al’ummar yankin ke yi masa.

A wata sanarwa da ya fitar, Usmaniyya ya ce ya yanke wannan shawara ne bisa kishin al’umma da ƙudurinsa na wakiltar muradun jama’a cikin gaskiya, tare da kare haƙƙoƙinsu da kuma tabbatar da cigaba mai ɗorewa.

Yadda Cacar Zamani Ke Lalata Rayuwar Matasan Arewacin Nijeriya

Advertisement

Ya bayyana cewa yana da yakinin cewa haɗin kai, addu’a da goyon bayan al’umma za su taimaka wajen samar da wakilci nagari a Akko ta Arewa.

Usman Abubakar Usmaniyya ya kuma miƙa kansa ga al’ummar yankin domin neman cikakken goyon bayansu, yana mai addu’ar Allah Ya sanya wannan takara ta zama alkhairi ga yankin baki ɗaya.

Sanarwar ta samu sa hannun Magatakarda, Alamin Sirajo Bappah, Usman Abubakar Usmaniyya (Tauraron Gona)

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *