Connect with us

News

Yadda Cacar Zamani Ke Lalata Rayuwar Matasan Arewacin Nijeriya

Published

on

1690373875944
Spread the love

Caca na ƙara yaɗuwa a tsakanin matasan Arewacin Nijeriya duk da haramci da gargadin addini, lamarin da ke jefa matasa cikin talauci da matsalolin rayuwa.

A da, ana gudanar da caca ne a fili ta hanyar katin wasa, inda galibi matasa da marasa aikin yi ke taruwa. Sai dai a wannan zamani na fasahar intanet, wayoyin hannu sun ba masu caca damar gudanar da harkarsu a ɓoye, ba tare da sanin iyaye ko al’umma ba.

Masana sun danganta wannan yanayi da tsananin talauci, rashin aikin yi, da yawaitar amfani da wayoyin smartphone.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa talauci ya kai kashi 77.7 cikin 100 a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, abin da ke tura wasu matasa neman hanyoyin samun kuɗi cikin sauri, ciki har da caca kamar yanda Jaridar LEADSHIP ta ruwaito

Yadda Cacar Zamani Ke Lalata Rayuwar Matasan Arewacin Nijeriya

Sha’awar kallon wasannin ƙwallon ƙafa, musamman gasar English Premier League, ta zama hanyar da kamfanonin caca ke amfani da ita wajen jawo hankalin matasa. Wasu daga cikinsu na ganin cewa saninsu kan ƙwallon ƙafa zai ba su damar cin riba, duk da cewa galibi sakamakon ya kan zama asara.

Advertisement

A jihar Kano, inda dokar Shari’ar Musulunci ta haramta caca tun shekarar 2000, Hukumar Hisbah na ci gaba da kai samame kan shagunan caca. Duk da haka, harkar na ci gaba da bunƙasa ta kafafen intanet, abin da ke sa hukumomi fuskantar ƙalubalen dakile ta gaba ɗaya.

Kididdiga ta nuna cewa zuwa ƙarshen shekarar 2025, kasuwancin caca a Nijeriya ya kai kusan dala biliyan 3.63, kwatankwacin sama da naira tiriliyan 5.6. Masana na gargadi cewa caca na ƙara jefa matasa cikin talauci maimakon magance matsalolinsu.

Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya ce, “Caca haramun ce a Musulunci kamar yadda shan giya yake haramun. Abin takaici ne yadda wasu matasa suka daina sana’o’i suka dogara kacokan kan caca. Wannan na iya haifar da matsaloli da dama, ciki har da aikata laifuka da shaye-shaye.”

Advertisement

Ya ƙara da cewa, “Muna kira ga iyaye da shugabannin al’umma su sa ido sosai kan yadda matasa ke amfani da wayoyin hannu da intanet. Ayyukan wayar da kai da tsauraran matakai daga hukumomi ne kadai zai rage wannan mummunar dabi’a.”

Dr. Mujahideen ya kuma jaddada cewa an ƙirƙiro wasu wasannin caca ne da nufin lalata makomar matasa, lamarin da ke jawo su zuwa aikata laifuka ko shaye-shaye.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *