News
Gwamnan Katsina Zai Gina Gidaje 3,750 A Radda Da Kankiya Kan Naira Biliyan 155
Gwamnan Katsina zai gina gidaje 3,750 a mahaifarsa Radda da Kankiya mahaifar ministan gidajen Najeriya kan kudi naira biliyan 155
Mataimaki na musamman ga gwamnan Umaru Radda kan kafafen watsa labaru MS Ingawa a wata sanarwa da ya fitar, ya ce tuni aka saka hannu a kan yarjejeniyar gina gidajen da wani kamfani ,mai suna COSMOS Residential City Nigeria Limited.
Zaɓen 2027: Matashin dan jarida Ya amsa kiran al’ uammar Akko ta Arewa
Gwamnan ya bayyana cewa 2,500 gidaje za a gina a Kankiya, yayin da 1,250 za su kasance a Radda, Charanchi LGA.
A karkashin wannan shiri, kowanne gida zai samu noman kifi da lambun kayan marmari, domin tallafawa iyalai da samar da kudin shiga.
Shirin zai dauki watanni 16 zuwa shekaru 2, inda gwamnati ta riga ta ware fili kuma za ta gano matasa marasa aiki da iyalai masu karamin karfi da za su amfana.
Kowanne mai amfana zai iya samun har N200,000 a wata, tare da ajiyar kudi tsakanin N50,000 zuwa N70,000 don rage bashin masu zuba jari. Bayan shekaru 3 zuwa 5, gidaje da gonaki za su zama mallakar masu amfana gaba daya..
