Connect with us

News

Gwamnatin Tarraya Ta Musanta Zargin Biyan Kudin Fansa Don Ceto Ɗaliban Papiri

Published

on

014bb4152e28663712121e66534d12c70913e0603a838b77536899694b8706f1

Gwamnatin Tarayya ta musanta zarge-zargen da ke cewa ta biya “makudan kudaden fansa”, tare da sakin wasu kwamandojin ‘yan bindiga, domin samun ‘yancin daliban da aka sace daga makarantar kwana ta St. Mary’s da ke Jihar Neja.

A cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Talata, gwamnatin ta bayyana rahotannin, wadanda aka danganta su da wasu kafafen yada labarai na kasa da kasa a matsayin ƙarya marar tushe da kuma abin da zai iya ɓata martabar jami’an tsaro.

Advertisement

Dan Jarida Zai Kai Kara Kotu Biyo Bayan Cin Mutuncinsa Da Jami’in Gwamnatin Kano Ya yi ‎

Sanarwar ta ce babu wani kudin fansa da aka biya, kuma ba a saki wani kwamandan ‘yan bindiga ba dangane da aikin ceton daliban.

Advertisement

“Wadannan zarge-zarge ƙarya ne tsantsa, kuma suna tauye ƙwarewa da sadaukarwar da jami’an tsaronmu ke yi a kullum,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta soki rahotannin da cewa sun dogara ne kacokan kan wasu majiyoyi marasa suna da aka bayyana a matsayin “majiyoyin leƙen asiri” ko kuma “wadanda suka san yadda tattaunawar ta gudana,” maimakon bayanan hukuma da aka bayyana a fili.

Advertisement

Ta ce Ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da kuma shugabannin Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun fito ƙarara sun musanta batun biyan kudin fansa.

Sanarwar ta kuma bayyana zargin cewa an kai kudin fansa ta jirgin sama mai saukar ungulu ga ‘yan ta’adda, a matsayin kirkirarren labari. DSS ta bayyana wannan zargi a matsayin ƙarya marar tushe.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa an samu nasarar kubutar da daliban ne ta hanyar ƙwarewar leƙen asiri da kuma tsare-tsaren aiki na musamman, ba tare da rasa rai ba.

Ta kara da cewa Nijeriya na fuskantar wani tsararren harkar ta’addanci da aka mayar da ita hanyar neman kudi, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakai bisa doka domin tabbatar da tsaro.

Advertisement

Gwamnatin ta kuma bukaci kafafen yada labarai da su riƙa tantance gaskiya kafin wallafa rahotannin da ka iya ƙarfafa gwiwar masu aikata laifi ko kuma rage ƙwarin gwiwar jami’an tsaro.

 

Advertisement

TRT AFRIKA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending