News
Hassada Da Rashin Haɗin Kai Ne Ke Hana Arewacin Najeriya Ci Gaba —Alhaji Shehu Ashaka
Dattijon Arewacin Najeriya kuma fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Shehu Ashaka, ya bayyana cewa hassada da rashin haɗin kai su ne manyan dalilan da ke hana yankin Arewa samun ci gaba mai ɗorewa, tare da haddasa rushewar kyawawan al’adun zamantakewa.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da Muhasa TV and Radio, inda ya ce matsalolin da ake fuskanta a yau sun samo asali ne daga watsi da kyawawan ɗabi’u da tsoffin shugabanni suka gina al’umma a kansu.
Shugaban Tashar Dala FM Kano, Ahmad Gazzali Yakub , Ya Yi Murabus Daga Aikinsa
A cewarsa, a baya al’ummar Arewa na rayuwa cikin haɗin kai da mutunta juna, tare da fifita moriyar al’umma gaba ɗaya, amma yanzu waɗannan ginshiƙai sun yi rauni, abin da ya haifar da rabuwar kai da koma baya.
Alhaji Shehu Ashaka ya jaddada cewa mafita na nan idan al’umma suka dawo kan tafarkin gyaran halaye, suka dage da addu’a da neman gafarar Allah, tare da barin munanan ɗabi’u da ke kawo cikas ga cigaban yankin.
Ya kuma yi gargaɗin cewa muddin ba a sauya halin da ake ciki ba, ci gaban da za a samu ba zai wuce irin na mutum ɗaya ko ƙungiya kaɗan ba, maimakon ci gaban al’umma baki ɗaya.
