News
Mutum 4 Sun Mutu, 18 Sun Jikkata A Turmutsitsin Karbar Sadakar Ramadan A Katsina
Mutum hudu sun rasa rayukansu yayin da wasu 18 suka samu raunuka sakamakon turmutsitsi da ya barke a lokacin raba Zakkar Ramadan a birnin Katsina.
Shafin Zagazola Makama ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren Alhamis 26 ga Fabrairun 2026 a gidan Alhaji Dahiru Usman Sarki da ke unguwar Kofar Guga, inda aka shirya rabon zakkar shekara-shekara.
Muhimmancin Ciyarwa Da Ba Da Sadaka A Watan Ramadan
Rahotanni sun ce jama’a da dama ne suka taru domin karbar tallafin Ramadan, amma wasu daga ciki suka yi yunkurin kutsa kai cikin harabar gidan, lamarin da ya haddasa turmutsitsi.
Jami’in yansanda mai kula da babban ofishin yansanda na birnin Katsina ya garzaya wurin tare da jami’ansa, inda suka samu nasarar shawo kan cinkoson tare da dawo da zaman lafiya.
Sakamakon turmutsitsin, mutane 18 sun samu raunuka daban-daban, kuma an kai su Babban Asibitin Katsina domin samun kulawar likitoci, yayin da likita ya tabbatar da mutuwar mutane hudu daga cikinsu.
An bayyana sunayen wadanda suka rasu da suka hada da Bilkisu Mamman mai shekaru 40 daga unguwar Kerau, Ihsan Musbahu mai shekaru 40 daga Abattoir, Aisha Sani mai shekaru 16 daga Kofar Sauri da Salamatu Kabir mai shekaru 45 daga Sabuwar Unguwa.
Haka kuma, wata yarinya Hafsat Zubairu mai shekaru 15 daga unguwar Masanawa, an kai ta Asibitin Koyarwa na Tarayya domin duba ta.
Hukumomin yansanda sun ce sun gayyaci masu shirya rabon zakkar domin yi musu tambayoyi, yayin da bincike kan musabbabin faruwar lamarin ke ci gaba.
