News
Gwamnatin Jigawa Ta Tsige Alƙalin Kotun Musulunci Kan Rashawa
Hukumar Shari’ah ta Jihar Jigawa (JSC) ta amince da tilasta wa alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci da ke jihar yin ritaya.
Wannan na ƙunshe ne a wata takarda babban jami’in yaɗa labaran JSC, Abba Wangara ya fitar a yau Talata, a Dutse.
Haka kuma, hukumar ta amince da ƙarin matsayi ga wasu jami’anta guda 80 a muƙamai daban-daban.
Ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne yayin wani zama da hukuncin ta gudanar a Dutse.
A cewarsa, bayan bincike mai zurfi da samar da hujja mai ƙarfi akan ƙorafin da aka gabatar akan alƙalin, JSC ta yanke hukuncin tilasta wa Muhammad Haruna yin ritaya.
Ya ƙara da cewa, matakin ya biyo bayan miƙa ƙorafin ne da wani Abdullahi Hamza ya jagoranta, wanda ya yi sanadiyyar samun alƙalin da hannu a laifin rashawa da tsarewa ba bisa doka ba.
Wangara ya ce bincike ya nuna cewa alƙalin ya nemi wanda ya shigar da ƙorafin da biya wasu kuɗaɗe da ba sa bisa doka ba, don haka ya tilasta masa biyan wasu kuɗaɗe da tsare shi.
A watan Junairun 2025 ne JSC ta sallami jami’an shari’a bisa ayyukan saɓa wa dokokin aiki, shawartar wasu alƙalai uku da su yi murabus da kuma dakatar da wasu biyu daga aiki.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
