News
Gobara Ta Tashi A Kamfanin Ganyen Shayin Maya Dake Kano.
Wata gobara ta tashi a wani kamfanin sarrafa ganyen shayi mai suna Maya da ke yankin Sharada a Jihar Kano, kamar yadda Freedom Radio ta ruwaito.
Rahotanni sun ce gobarar ta ɓarke ne cikin dare, inda harshen wuta ya mamaye wasu sassan kamfanin, lamarin da ya jefa ma’aikata da mazauna yankin cikin fargaba.
Gawuna Ya Fice Daga Jam’iyyar APC
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa wutar ta bazu cikin sauri, ana danganta hakan da yanayin kayayyakin da ke cikin masana’antar.
Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan musabbabin tashin gobarar, haka kuma ba a tabbatar da ko an samu asarar rayuka ko kuma yawan barnar da aka yi ba.
Jami’an kashe gobara sun isa wurin domin kokarin shawo kan lamarin tare da hana wutar ƙara yaɗuwa.
Ana sa ran hukumomi za su fitar da ƙarin bayani a kan wannan lamari nan gaba kaɗan.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
