Connect with us

News

Hare-haren Ƴanbindiga Sun Yi Ajalin Mutane Aƙalla 60 A Jihohin Neja Da Kebbi

Published

on

Majiyoyi daga ƙungiyoyin agaji a Najeriya, sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, ƴanbingar waɗanda wasu ke da alaƙa da ƙungiyoyi masu ikirarin  jihadi, sun kai hare-hare da dama babu kakkautawa kan mazauna ƙauyukan a jihohin Neja da Kebbi makwabta, inda suka tilastawa sama da mutane 500 tserewa daga muhallansu.

Gwamnatin Tarraya Za Ta Fara Shari’ar Mutum 500 Da Ake Zargi Da Ta’addanci

Advertisement

Rahotanni na cewa, bayaga kisan mutane sama da 60, ƴan bindigar sun ƙone gidaje da dama, inda majiyoyin tsaro suka ɗaura alhaki kan mayakan Mahmuda masu ikirarin jihadi.

Majiyoyin sun ce, harin ranar Talata a Erena da ke ƙaramar hukumar Shiroro na jihar Neja, ya halla aƙalla mutane 20, ƴan sanda sun tabbatar da cewar mayakan sakai na vigilanti biyu da wani diren jami’an tsaro na ciki.

Advertisement

A jihar Kebbi kuwa, rahotanni na cewa aƙalla mutane 24 aka kashe, sai dai wata majiyar coci ta ce adaɗin waɗanda aka kashe ya kai 40.

Sun ce, mayakan basu nuna banbancin iddinin wajen kisan ba, la’akari da cewa, hare-haren sun rutsa na musulmi da kiristoci harma masu addinin gargajiya.

Advertisement

 

RFI

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending