News
Kaso 85 Na Mata Da Ƙananan Yara Na Mutuwa Sanadin Zazzaɓin Cizon Sauro — Rahoto
Babban Jami’in lafiya a matakin farko na Jihar Kano, Nasiru Abdulhamid, ya bayyana cewa kusan kashi 85 cikin 100 na mace-macen da cutar zazzabin cizon sauro (Malaria) ke haifarwa na shafar mata masu juna biyu da ƙananan yara.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar INDA RANKA, inda ya jaddada cewa waɗannan rukuni na al’umma su ne mafi rauni wajen fuskantar illar cutar, musamman a yankunan da ake fama da ƙarancin tsaftar muhalli.
A cewarsa, bayanai daga World Health Organization sun nuna cewa cutar Malaria na ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar al’umma a Afirka, inda yara ƙanana da mata masu juna biyu ke kan gaba wajen fuskantar haɗari.
Nasiru Abdulhamid ya danganta yawaitar cutar da rashin tsaftar muhalli, yana mai cewa taruwar ruwa a cikin kwantena, magudanan ruwa da suka toshe, da kuma yawaitar shara na samar da muhalli mai kyau ga sauro su hayayyafa.
Ya ƙara da cewa duk da matakan da ake ɗauka, har yanzu akwai buƙatar ƙara wayar da kai da kuma haɗin gwiwar al’umma domin rage yaɗuwar cutar.
Hukumomin lafiya sun shawarci jama’a da su riƙa tsaftace muhallansu, su rika amfani da gidajen sauro masu ɗauke da maganin kashe ƙwari, tare da gaggauta zuwa asibiti idan an fara jin alamun cutar.
Masana sun kuma yi kira ga gwamnati da ƙungiyoyin lafiya da su ƙara ƙaimi wajen samar da kayan rigakafi da magunguna masu inganci, domin kare rayuwar mata da ƙananan yara da ke cikin mafi haɗari.
