News
Shari’o’in Zaɓe: Kotu Ta Kawo Sabon Tsari Don Kauce Wa Ƙarewar Wa’adi
Babbar Kotun Tarayya ta Najeriya ta ba da umarnin fara karɓar ƙararrakin da suka shafi shari’o’in gabanin zaɓe a ranakun ƙarshen mako da kuma ranakun hutun musamman da gwamnati ke ayyanawa.
Wata sanarwa da Babban Magatakardan Kotun, Yahaya Shafa, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa masu ƙorafi da lauyoyinsu sun samu damar shigar da ƙararraki cikin wa’adin da doka ta tanada.
Sanarwar ta ce za a riƙa buɗe rajistar kotuna daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 2:00 na rana a ranakun Asabar da Lahadi, da kuma ranakun hutun da gwamnati ta ayyana.
Kotun ta ce manufar sabon tsarin ita ce kauce wa duk wani jinkiri da ka iya haifar da ƙarewar wa’adin shigar da ƙara, musamman a shari’o’in da suka shafi zaɓe, waɗanda doka ta ware musu takamaiman lokaci.
Matakin ya shafi shari’o’in da suka danganci zaɓukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa, rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyu da sauran batutuwan da suka shafi shirye-shiryen zaɓukan da ke tafe.
Masu sa ido kan harkokin shari’a na ganin cewa matakin zai taimaka wajen sauƙaƙa wa masu neman adalci da kuma tabbatar da cewa babu wanda zai rasa damar gurfanar da ƙorafinsa saboda ranakun hutu.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News5 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
