News
Mutuwar Ɗalibi Kan N13,500 Ta Jawo Dakatar Da Karatu Da Zanga-Zanga A Jami’ar FUTO
Ƙungiyar Daliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) a Jihar Imo ta sanar da dakatar da dukkan harkokin karatu na tsawon mako guda bayan mutuwar wani ɗalibi sabon ɗauka, Chinedu Christogonus, a wani yanayi da ya haifar da ce-ce-ku-ce a harabar jami’ar.
Matakin na zuwa ne yayin da ɗalibai ke ci gaba da nuna fushinsu tare da neman a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin mutuwar marigayin.
Jami’an DSS Sun Cafke Mutum 5 Ciki Har da ‘Yan Kasar Waje Kan Zargin Sace Ɗalibai A Neja
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga wata takaddama kan kuɗi Naira 13,500 da ake zargin an samu daga wani aikin sintiri. Marigayin, wanda ɗalibi ne a fannin Cybersecurity, ana zargin ya yi amfani da kuɗin wajen sayen littattafan karatu.
Wasu majiyoyi daga jami’ar sun ce bayan dawowarsa daga wani taro a Jihar Abia, an nemi ya yi bayani kan kuɗin, inda daga bisani aka hukunta shi mai tsanani.
Shaidu sun bayyana cewa duk da roƙon wasu ɗalibai da masu wucewa da a dakatar da hukuncin, an ci gaba da yi masa azaba na sa’o’i da dama har ya suma.
An garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Owerri domin ceto rayuwarsa, sai dai an tabbatar da mutuwarsa bayan isa asibitin.
Mutuwar tasa ta haddasa zanga-zanga a cikin jami’ar, inda ɗalibai suka fito suna neman adalci ga abokinsu. Rahotanni sun ce yayin zanga-zangar an samu lalata wasu kayayyaki da gine-ginen jami’ar sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan lamarin.
A wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar Dalibai (SUG), Christopher Chukwuebuka, da Babban Sakataren ƙungiyar, Mark Christopher, suka sanya wa hannu, an sanar da dakatar da dukkan laccoci, gwaje-gwaje da sauran harkokin ilimi daga ranar Litinin, 1 ga Yuni zuwa Juma’a, 5 ga Yuni, 2026.
Ƙungiyar ta ce matakin ya zama dole domin matsa lamba ga mahukuntan jami’ar su bayyana gaskiyar abin da ya faru, tare da fayyace matakan da ake ɗauka wajen gudanar da bincike da tabbatar da adalci.
Ta kuma buƙaci ɗalibai su kasance masu bin doka da oda yayin da ake ci gaba da neman hukunci ga waɗanda ke da hannu a lamarin.
A gefe guda kuma, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo ta tabbatar da cafke wasu ɗalibai uku bisa zargin hannu a mutuwar marigayin.
Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya ce binciken farko ya nuna cewa an tsare matashin tare da yi masa mummunan duka wanda ya janyo masa raunukan da suka yi sanadin mutuwarsa.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Chukwuemeka Benedict mai shekaru 21, Kelechi Gospel Ikenna mai shekaru 24 da Obioma Anastasia mai shekaru 21, waɗanda dukkansu ɗaliban Shekarar Ƙarshe ne a jami’ar.
Rundunar ’yan sandan ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan lamari.
