Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Matashin Da Ya Hallaka Mahaifinsa

Published

on

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo ta cafke wani mutum mai shekara 38 da haihuwa, Nsikak Kingsley, bisa zargin dukan mahaifinsa har lahira bayan wata takaddama da ta kaure a tsakaninsu a garin Oda da ke Ƙaramar Hukumar Akure ta Kudu.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abayomi Jimoh, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Advertisement

Hatsarin Mota Ya Hallaka Jami’in Soja Da Masu Yi Wa Ƙasa Hidima 4 A Adamawa

A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 28 ga Mayu, 2026, lokacin da wata muhawara ta rikide zuwa rikici tsakanin wanda ake zargin da mahaifinsa, Adone Peter, mai shekara 65.

Advertisement

Jimoh ya ce rikicin ya kai ga faɗa, inda marigayin ya samu munanan raunuka a jikinsa, musamman a kai, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti domin ceto rayuwarsa.

Sai dai duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi, marigayin ya rasu yayin da ake kula da lafiyarsa.

Advertisement

Sanarwar ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ondo, CP Felix Ohagwu, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin tabbatar da adalci.

“Bayan samun rahoton korafi daga ɗan’uwan wanda ake zargin a wani ofishin ’yan sanda da ke yankin, jami’ai suka gaggauta ɗaukar mataki, inda suka kama wanda ake zargin domin ci gaba da bincike,” in ji sanarwar.

Advertisement

Rundunar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike, yayin da ake sa ran gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Lamarin ya sake tayar da hankalin jama’a kan yadda rikice-rikicen cikin gida ke ƙara haddasa asarar rayuka a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Advertisement

A wani lamari makamancin wannan da ya faru a shekarar 2024, rundunar ’yan sanda a Jihar Legas ta kama wani matashi mai shekara 25, Chibunnma Chimelie, bisa zargin caka wa mahaifinsa mai shekara 68 wuka har ya mutu a yankin Isolo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending