Connect with us

News

Hatsarin Mota Ya Hallaka Jami’in Soja Da Masu Yi Wa Ƙasa Hidima 4 A Adamawa

Published

on

adamawa accident (1)

Wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Jihar Adamawa ya yi sanadin mutuwar mutane shida, ciki har da wani jami’in soja da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) guda huɗu.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne lokacin da motar da mamatan ke ciki ta yi haɗari da wata mota, lamarin da ya janyo tashin gobara mai ƙarfi wadda ta cinye motar gaba ɗaya.

Advertisement

Yadda Faɗan Daba Ya Jefa Al’ummar Kawo Cikin Firgici A Kano

Shaidu sun ce motar ta kama da wuta nan take bayan haɗarin, abin da ya hana fasinjojin da ke cikinta samun damar tsira daga gobarar. Dukkanin mamatan sun rasa rayukansu a wurin da lamarin ya faru.

Advertisement

Jami’an agajin gaggawa tare da hukumomin tsaro sun isa wurin domin gudanar da ayyukan ceto, da kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu, tare da daidaita zirga-zirga a yankin.

Bayanan farko sun nuna cewa masu yi wa ƙasa hidimar na kan hanyarsu ne lokacin da hatsarin ya afku, sai dai har yanzu hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan musabbabin aukuwar lamarin ba.

Advertisement

An kuma fara gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa hatsarin da ya jawo wannan mummunar asarar rayuka.

Lamarin ya jefa iyalan mamatan da al’ummar yankin cikin alhini da jimami, yayin da hukumomi suka sake jan hankalin masu ababen hawa da su kiyaye dokokin hanya tare da kauce wa tuki cikin ganganci domin rage yawaitar hatsarurrukan da ke salwantar da rayuka a sassan ƙasar nan.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Channelstv

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending