News
Yadda Faɗan Daba Ya Jefa Al’ummar Kawo Cikin Firgici A Kano
Mazauna unguwar Kawo da ke cikin birnin Kano na ci gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon rikicin faɗan daba da ya ɗauki kwanaki uku ana yi ba tare da katsewa ba, lamarin da ya haddasa tashin hankali tare da kawo cikas ga harkokin yau da kullum a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya tilasta wa wasu ‘yan kasuwa rufe wuraren sana’arsu, yayin da masu ababen hawa da sauran matafiya suka fara kauce wa yankin saboda tsoron fadawa cikin hatsari.
Matashi Ya Rasa Ransa Yayin Kokarin Nuna Bajinta Ga Budurwarsa
Wasu mazauna unguwar sun shaida cewa rikicin ya yi matuƙar shafar harkokin kasuwanci da zamantakewa, tare da jefa al’umma cikin damuwa da rashin tabbas kan tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.
A cewar mazauna yankin, rikicin ya samo asali ne tun kusan makonni uku da suka gabata bayan wata takaddama da ta ɓarke tsakanin wasu ‘yan adaidaita sahu. Daga baya, lamarin ya rikide zuwa ramuwar gayya tsakanin wasu ƙungiyoyi da ake zargin na ‘yan daba ne.
Shaidu sun ce tashin hankalin ya ƙara kamari ne lokacin da wani ɓangare ya tare hanya da sassafe, abin da ya haddasa arangama mai tsanani, tare da jikkatar mutane da lalata wasu ababen hawa.
Tun daga wannan lokaci, rahotanni ke nuna cewa ɓangarorin biyu na ci gaba da kai wa juna hare-hare, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin.
Wasu mazauna Kawo sun bayyana halin da ake ciki a matsayin abin damuwa, suna mai cewa yawaitar matasa masu ɗauke da makamai a tituna ya sanya zirga-zirga da gudanar da harkokin yau da kullum cikin haɗari.
Wani ɗan gwagwarmayar al’umma a Kano ya danganta rikicin da matsalar yawaitar shan miyagun ƙwayoyi da kuma tasirin siyasa, yana mai kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen faɗan daba da ke addabar matasa.
A nasa ɓangaren, jami’an tsaro sun tabbatar da cewa suna sane da lamarin kuma sun fara ɗaukar matakan da suka dace domin dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai duk da wannan tabbacin da hukumomin tsaro suka bayar, mazauna yankin sun ce har yanzu suna cikin firgici, yayin da ba a fitar da sahihin adadin mutanen da suka jikkata sakamakon rikicin ba.
