News
Wani Mutum Ya Rasa Ransa Wajen Dauko Wata Waya Da Ta Fada Rijiya A Kano
Wani mutum mai shekaru 45, Yusuf Usman, ya rasu bayan ya shiga wata tsohuwar rijiya domin ciro wayarsa da ta faɗa ciki a ƙauyen Kwa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:13 na safiyar ranar Laraba, inda nan take ta tura tawagar ceto zuwa wurin da lamarin ya faru.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce da isar jami’anta wurin, sun tarar da mutumin a cikin rijiyar da aka daina amfani da ita, wadda daga bisani aka mayar wurin zubar da shara.
Jami’an ceto sun samu nasarar fito da shi daga cikin rijiyar cikin halin suma, amma daga baya aka tabbatar da rasuwarsa.
Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya rasa ransa ne sakamakon ƙarancin iskar shaƙa da kuma tsananin zafin da ke cikin rijiyar.
Hukumar ta ce an miƙa gawarsa ga Hakimin ƙauyen Kwa, Alhaji Muktar, domin ci gaba da shirye-shiryen jana’izarsa.
Da yake martani kan aukuwar lamarin, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ya yi kira ga jama’a da su tabbatar da rufe rijiyoyin da aka daina amfani da su tare da cike su yadda ya kamata domin kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma buƙaci iyaye, shugabannin al’umma da masu unguwanni da su ƙara himma wajen kula da muhallansu domin hana afkuwar irin waɗannan munanan haɗurra.
