News
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Masu Aikata Muggan Laifuka Sama Da 300 A Kano
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta kama mutane 345 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da kwato makamai 270 a wani samame na kwana uku da ta gudanar a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Bakori, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Litinin, inda ya ce samamen na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka domin ƙarfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
MAN FETUR: Sama Da Kaso 70% Na Kuɗin Shiga Na Masu Adaidaita Sahu Na Narkewa A Sayen Mai — Rahoto
A cewarsa, an fi mayar da hankali ne kan ’yan daba, dillalan miyagun ƙwayoyi da masu mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, domin dakile safarar miyagun kwayoyi da hana aukuwar rikice-rikice a sassa daban-daban.
Ya ce wannan aiki ya gudana ne cikin nasara, inda aka cafke mutane da ake zargi da fashi da makami, ’yan daba da kuma masu safarar kwayoyi, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
Rundunar ta kuma bayyana cewa ta kwato makamai 270 da suka haɗa da wukake, adduna, kulake da sauran kayan da ake amfani da su wajen tayar da tarzoma.
Haka kuma, an gano nau’ikan miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da tabar wiwi, allunan Exol da kuma wani sinadari mai haɗari da aka fi sani da “Suck and Die.”
Kwamishinan ya ce wannan nasara ta taimaka matuƙa wajen rage ƙarfin masu aikata laifuka da hana su ci gaba da tada hankali a cikin al’umma.
Ya ƙara da cewa Operation Kukan Kura na ci gaba da aiki a faɗin jihar, inda ake ƙara ƙarfafa sintiri da hanzarta kai ɗauki ga rahotannin gaggawa.
A cewarsa, sabuwar sashen rundunar mai suna Violent Crime Response Unit ta ƙara inganta saurin martani kan bayanan sirri da ke alaƙa da ayyukan tashin hankali.
Rundunar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kai samame da gurfanar da duk wanda aka kama, domin tabbatar da cewa Kano ta samu cikakken zaman lafiya mai ɗorewa.
