News
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Mutum Da Wayoyin Sata Guda 36
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya ta ce ta kama wani mutum mai suna Musa Idris da ake zargi da karɓa da kuma safarar wayoyin hannu da aka sace.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Baba Azare, ya shaida wa manema labarai a birnin Uyo cewa jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri kan wani hari na fashi da makami da aka kai a kan hanyar Calabar zuwa Itu.
A cewarsa, an samu wayoyin Android guda 34 da kuma wayoyi ƙirar button guda biyu a hannun Musa Idris, waɗanda ake kyautata zaton an samo su ne daga ayyukan fashi da makami.
Akwai Yiwuwar Ƙara Kuɗin Kiran Waya Da Aika Saƙo A Najeriya
Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa an taɓa kama wanda ake zargin a watan Oktoban shekarar 2025 bisa zargin hannu a ayyukan fashi da makami da kuma mallakar sama da wayoyin hannu 200 da ake zargin na sata ne.
Kwamishinan ya ce bayanan farko da aka samu daga wanda ake zargin sun nuna akwai wata hanyar sadarwa ta masu safarar wayoyin sata da ke aiki a sassa daban-daban na Najeriya, har ma da wajen ƙasar.
Ya ƙara da cewa rundunar ta fara ƙoƙarin gano tare da kama sauran waɗanda ake zargi da hannu a wannan lamari.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News4 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
