Connect with us

News

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu mutane hudu da ake zargi da satar shanu da awaki

Published

on

Dan sanda

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu mutane da ake zargin sun kware wajen satar shanu da awaki a garin Maigari.

Advertisement

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Shiisu Adam, mataimakin Sufeton ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Dutse, babban birnin jihar.

Tinubu na duba yiwuwar dawo da tallafin man fetur na wucin gadi.

Adam ya ce yayin da aka kama wasu mutum biyu da ake zargi da sata shanu,haka kuma an kuma kama wasu biyu da awakin sata.

Advertisement

Ya ce, “A ranar 2 ga Agusta, 2023, da misalin karfe 10 na dare, bayan samun rahoton wani Abdullahi Ya’u a.k.a Mado mai shekaru 20 a Bakin-Kara quarters da Nasiru Yusuf a.k.a Danlin mai shekaru 23 a Kofar-Arewa, duk An kama na garin Maigatari ne a wani gini da ba a kammala ba a unguwar Abuja, cikin garin Maigatari bayan sun yanka wani shanu da ake zargin an sace da kuma wani ba a yanka ba.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce an kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi, Buba Ahmadu, Adam Ahmadu da Haruna Ahamadu dukkansu mazauna Sabon Garin Walawa Fulani a karamar hukumar Birniwa, da bindigar Dane daya, bindigar gida daya da kuma baka da kibiya.

Advertisement

Ya kara da cewa, a ranar Litinin din da ta gabata, rundunar ta samu labarin cewa wasu mutane sun gano wata waya ta wutar lantarki da ke baiwa makarantar Tsangaya wuta a karamar hukumar Buji.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Punch

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending