News
An Kama Jami’an NSCDC Da Wani Mutum Guda Bisa Haɗin Baki Suna Yi Wa Ƴan Bindiga Safarar Makamai
Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta cafke wasu jami’an Hukumar Tsaro da Kariya ta Fararen Hula (NSCDC) biyu da wani jami’in Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya bisa zargin hannu a wata hanyar safarar makamai ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka a yankin Kudu maso Gabashin ƙasar.
Sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa kamen ya biyo bayan jerin hare-haren da dakarun Joint Task Force South East Operation UDO KA suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Kwamitin Ƙwadago Ya Ƙara Ƙaimi Kan Rijistar Katin Zaɓe, Daruruwa Sun Yi Rijista a Hotoro
Waɗanda aka kama sun haɗa da Mataimakin Sufeto na NSCDC, Obaji Sampson, Sufeto Tasie Victor Nnamdi, wanda ke kula da rumbun makamai na rundunar a Jihar Enugu, da kuma Mataimakin Sufeton Hukumar Gidajen Gyaran Hali, Ekwueme Onyebuchi Clement.
A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa Tasie Victor Nnamdi shi ne babban wanda ake zargi da samar da makaman, yayin da Ekwueme Onyebuchi Clement ke cikin manyan waɗanda ake zargin suna karɓa da rarraba su ga masu aikata laifuka.
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan samun ƙarin bayanan sirri, sojoji sun kai samame wani gida da ke Achara Road, Trans-Ekulu Golf Estate a Jihar Enugu, inda suka kama wani da ake zargi mamba ne na ƙungiyar IPOB/ESN, mai suna Friday Nnanna, wanda ake zargin yana safarar makamai.
A yayin samamen, an ƙwato harsasai 247 na bindigar 7.62mm, harsasai 12 na bindigar 9mm, harsasai 29, bindigogi huɗu ƙirar Pump Action, bindigar Beretta guda ɗaya, faranti daban-daban na motoci, kayayyakin haɗa bam na IED, takubba iri-iri, hayaki mai sa hawaye (tear gas), kayan aikin soja da kuma motoci huɗu.
Hakazalika, a wani samame da aka gudanar a Jihar Cross River tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), an kama wasu mutum uku tare da ƙwato bindigogi ƙirar Dane guda biyu, bindiga ƙirar gida guda ɗaya, harsasai shida, kayan aikin soja da wasu abubuwan da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan ta’addanci.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce waɗanda aka kama da duk kayayyakin da aka ƙwato suna ci gaba da kasancewa a hannunta domin zurfafa bincike.
Ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da hare-haren da suka dogara da bayanan sirri tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin lalata hanyoyin da masu aikata laifuka ke samun makamai, da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar.
-
News4 days ago
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Basarake Bisa Zargin Kona Wani Mutum Kan Zargin Satar Itacen Girki
-
News3 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Bada Umarnin Binciken Kuɗaɗen Tsaro Na Ƙananan Hukumomi 44 Cikin Mako Biyu
-
News1 day ago
Shugaban FCAPT: Rajistar Katin Zaɓe Muhimmin Mataki Ne Wajen Ƙarfafa Dimokuraɗiyya
