Connect with us

News

One Kano Agenda Ta Roki Majalisar Dokokin Kano Ta Binciki Gwarzo Kan Zargin Karkatar Da Naira Miliyan 308

Published

on

images (9)

 

 

Wata ƙungiyar farar hula mai suna One Kano Agenda (OKA) ta buƙaci Majalisar Dokokin Jihar Kano da ta gudanar da bincike kan tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a da suka kai Naira miliyan 308 da aka ce an ware domin gudanar da addu’o’i na musamman a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Buƙatar na ƙunshe ne cikin wata takardar ƙorafi da ƙungiyar ta miƙa wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, wadda Darakta Janar na ƙungiyar, Ambasada Abbas Abdullahi Yakasai, ya sanya wa hannu.

Dakarun Soji Sun Hallaka Yanta’adda 662, Sun Ceto 951 Da Aka Sace Cikin Watanni Uku

A cewar ƙungiyar, matakin ya biyo bayan kalaman Mai Bai Wa Gwamnan Kano Shawara kan Harkokin Tsangaya, Sheikh Musa Falaki, wanda ya yi zargin cewa an karkatar da kuɗaɗen da aka fitar domin shirin addu’o’in na tsawon watanni bakwai.

Advertisement

Takardar ƙorafin ta bayyana cewa an yi zargin kowace daga cikin ƙananan hukumomi 44 ta riƙa bayar da Naira miliyan 44 a kowane wata domin gudanar da addu’o’in, waɗanda aka ce Sheikh Musa Falaki da Sheikh Ibrahim Sheshi Maihula ne za su jagoranta.

Sai dai, a cewar ƙungiyar, malaman addinin sun bayyana cewa ba su karɓi wani kuɗi da ya shafi shirin ba, kuma ba su gudanar da addu’o’in da aka ce an ware kuɗaɗen domin su ba.

OKA ta ce hakan ya haifar da zargin cewa an fitar da kuɗaɗe har Naira miliyan 308 ba tare da waɗanda aka ce za su aiwatar da shirin sun sani ko sun shiga cikinsa ba.

Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa lamarin na iya kasancewa cikin wani faɗaɗɗen bincike da ya shafi yadda aka tafiyar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar, inda ake zargin akwai wasu ɗaruruwan miliyoyin nairori da ke buƙatar bincike.

Dangane da haka, OKA ta roƙi Majalisar Dokokin Jihar Kano da ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa, tare da gayyatar tsohon Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, jami’an Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON), Sheikh Musa Falaki, Sheikh Ibrahim Sheshi Maihula da kuma jami’an Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano domin ba da bayanai kan lamarin.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci Majalisar ta tantance adadin kuɗaɗen da ake magana a kai, ta binciki ko an bi ƙa’idoji wajen amincewa, fitarwa da amfani da su, sannan ta ba da shawarar ɗaukar matakan shari’a idan bincike ya tabbatar da aikata wani laifi. Ta kuma buƙaci a kwato duk wata kadarar gwamnati da aka tabbatar an karkatar da ita bisa tanadin doka.

Advertisement

Sai dai ƙungiyar ta jaddada cewa ƙorafin nata ba yana nufin yanke hukunci kan kowane mutum ba ne, illa kira ne na tabbatar da gaskiya, riƙon amana da bin doka domin ƙarfafa amincewar al’umma ga cibiyoyin gwamnati.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending