Connect with us

News

An Kama Wani Mutum Bisa Zargin Sayar Da Ɗan Abokinsa Kan Naira Miliyan 1.3

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Najeriya sun kama wani mutum mai suna Sunday Onome bisa zargin safarar yara, bayan ya amsa cewa ya sayar da ɗan abokinsa kan kuɗi Naira miliyan 1.3.

An kama wanda ake zargin ne a garin Onitsha da ke Jihar Anambra tare da budurwarsa da kuma ɗansa, yayin wani samame da jami’an tsaro suka kai, wanda ya kai ga ceto wasu yara biyu da ake zargin ana shirin safarar su.

‎Sarkin Gaya Ya Umarci Hakimai Su Wayar da Kan Jama’a Kan Muhimmancin Katin Zaɓe ‎

Bayanan da ’yan sanda suka fitar sun nuna cewa Sunday Onome ya bayyana a yayin bincike cewa ya shiga harkar safarar yara ne bayan ya rasa aikinsa na tuƙi. Ya ce tun daga lokacin ya gudanar da safarar yara fiye da sau ɗaya, inda yake samun kuɗaɗe daga wannan haramtacciyar harka.

Wanda ake zargin ya kuma yi ikirarin cewa budurwarsa da ɗansa suna taimaka masa wajen kai yaran zuwa wuraren da aka umarce su, kafin daga bisani a miƙa su ga waɗanda ake zargin masu karɓar yaran ne.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun cafke mutanen ne a wani otal da ke Onitsha kafin a kammala miƙa yaran ga waɗanda ake zargin za su karɓe su.

Advertisement

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ake zargin suna da hannu a wannan harka, tare da tantance sahihancin bayanan da wanda ake zargin ya bayar.

’Yan sanda sun jaddada cewa za su ci gaba da yaƙi da safarar yara da sauran manyan laifuka, tare da gurfanar da duk wanda bincike ya tabbatar yana da hannu a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending