News
Sarkin Gaya Ya Umarci Hakimai Su Wayar da Kan Jama’a Kan Muhimmancin Katin Zaɓe
Mai Martaba Sarkin Gaya, Dakta Ali Ibrahim Abdulkadir, ya yi kira ga al’ummar Masarautar Gaya da su rungumi rajistar katin zaɓe tare da tabbatar da mallakarsa, yana mai jaddada cewa katin zaɓe shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyya kuma hanya mafi inganci ta zaɓen shugabanni nagari.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Ƙaramin Kwamitin Kartakwana kan Rajistar Katin Zaɓe (CVR) na Ɗan Malikin Kano, Kwamared Auwalu Mudi Yakasai, wanda ya jagoranci tawagar kwamitin zuwa masarautar domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin katin zaɓe.
An Tsinci Gawar Wani Matashi Da Aka Yi Wa Yankan Rago A Kano
Tun da farko, Kwamared Auwalu Mudi Yakasai ya ce kwamitin ya samu gagarumin goyon baya daga masarautun a faɗin jihar, yana mai bayyana cewa sarakuna na taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙonnin ci gaba ga al’umma.
Ya ce kwamitin ya lura cewa haɗin kan da ake samu daga sarakuna ya ƙara ƙarfafa gangamin wayar da kai kan rajistar katin zaɓe, domin katin zaɓe shi ne haƙƙin kowane ɗan ƙasa kuma makamin tabbatar da shugabanci nagari.
A cewarsa, mallakar katin zaɓe na bai wa ɗan ƙasa damar zaɓar shugabannin da yake da yaƙinin za su kare muradunsa tare da kawo ci gaba, yana mai ƙara da cewa dimokuraɗiyya ba za ta bunƙasa ba idan jama’a ba su fito sun yi rajista tare da amfani da katunansu wajen zaɓe ba.
Da yake nasa jawabin, Sarkin Gaya ya ce ya zama wajibi kowane ɗan ƙasa da ya cancanta ya mallaki katin zaɓe, domin ita ce hanya mafi dacewa ta tabbatar da shugabanci nagari, adalci da ci gaban al’umma.
Sarkin ya kuma umarci dukkan hakimai da masu unguwanni da ke ƙarƙashin Masarautar Gaya da su ƙara himma wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin rajistar katin zaɓe da kuma fitowa domin kaɗa ƙuri’arsu a lokacin zaɓe.
Hakazalika, ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa kafa Kwamitin Kartakwana kan Rajistar Katin Zaɓe (CVR), yana mai cewa wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen ƙara wayar da kan al’umma da ƙarfafa tubalan dimokuraɗiyya a Jihar Kano.
