Connect with us

News

Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano 

Published

on

Justice Watch NewsDije Audu Aboki (1)

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta tilasta wa wani alƙalin Kotun Shari’a ritaya bayan bincike ya same shi da laifin karɓar cin hancin Naira 250,000, tare da ladabtar da wasu ma’aikatan kotu saboda laifukan rashin ɗa’a.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar, ya ce an ɗauki matakan ne a taro na 90 na hukumar da aka gudanar ranar 3 ga Yulin 2026, bayan nazarin rahotannin kwamitin da ke binciken ƙorafe-ƙorafen da ake kai wa kan alƙalai da ma’aikatan kotu.

Za a gudanar da addu’o’in cika shekara da rasuwar Buhari a ranar Litinin

Sanarwar ta ce Alƙali Aliyu Yahaya Muhammad na Kotun Shari’a ta Babeji ne aka tilasta wa ritaya bayan bincike ya tabbatar da cewa ya karɓi cin hancin Naira 250,000 a wata shari’a mai lamba CV/474/2024 tsakanin Talatu Ibrahim da Muntari Abubakar Baguda.

Hukumar ta kuma umarce shi da ya mayar da kuɗin da aka ce ya karɓa.

A wannan shari’ar, magatakardan kotun, Ibrahim Ahmad Ibrahim, an dakatar da shi na tsawon watanni huɗu ba tare da albashi ba, bayan ya amsa cewa ya karɓi wani ɓangare na kuɗin cin hancin.

Advertisement

Haka kuma, hukumar ta tilasta wa Muzambilu Ado, Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kididdiga na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a, ritaya bayan bincike ya gano cewa ya samu aikin ne ta hanyar amfani da takardun shaidar karatu na bogi.

Bugu da ƙari, hukumar ta rage wa Alƙali Usman Haruna Usman na Babbar Kotun Shari’a ta Goron Dutse matsayi da daraja guda saboda sakaci da ya yi a wani lamari da ya jawo asarar kuɗin masu ƙara.

Har ila yau, ta tabbatar da dakatarwar shekara guda da aka yi masa daga gudanar da aikin shari’a tare da yi masa gargaɗi mai tsanani.

Baba Jibo Ibrahim ya ce waɗannan matakan sun nuna ƙudirin Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Kano na tabbatar da gaskiya, riƙon amana da ɗa’a a aikin shari’a.

Ya ƙara da cewa duk wani jami’in shari’a ko ma’aikacin kotu da aka samu da hannu a cin hanci, rashin ɗa’a ko amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba zai fuskanci hukuncin da ya dace.

 

Advertisement

JUSTICE WATCH NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending