Connect with us

News

Mata Huɗu Sun Haihu A Cikin Adaidaita Sahu Sakamakon Watsi Da Aikin Titin Yandodo Zuwa Mai-Allo A Kano

Published

on

Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Yi Tafiya, Yayin Da Rikici Ke Ƙara Tsamari A Jami’yyar NNPP A Kano

Mazauna yankunan Yandodo, Mai-Allo, Oromi, Mariri, Yargana da Tsamiya Babba da ke ƙananan hukumomin Nassarawa, Kumbotso da Gezawa a Jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta cigab da  aikin  titin Yandodo–Mai-Allo–Oromi–Mariri, suna zargin cewa jinkirin aiwatar da aikin na ci gaba da jefa dubban al’umma cikin mawuyacin hali.

Rahotanni na nuni da cewa duk da gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar aikin tun a watan Oktoban shekarar 2025 tare da kafa allon aikin a wurin, har yanzu ba a fara cikakken aikin ginin titin ba. Sun ce lalacewar hanyar, wadda ta cika da manyan ramuka da zaizayar ƙasa tare da yawaitar ambaliya a lokacin damina, na hana zirga-zirga cikin sauƙi tare da jefa rayukan mata masu juna biyu da marasa lafiya cikin haɗari.

IMG 20260708 WA0001

Rikici Ya Barke A Majalisar Wakilai Kan Buƙatar Gayyatar Shugaba Tinubu

Direban adaidaita sahu, Adamu Alhassan, ya shaida wa Global Tracker cewa mata masu juna biyu huɗu sun haihu a cikin babur ɗinsa a lokuta daban-daban saboda rashin yiwuwar isa asibiti cikin lokaci sakamakon munin hanyar.

A cewarsa, idan naƙuda ta tsananta yayin tafiya, yakan tsaya a wani wuri mai aminci domin ba matar kariya har sai ta haihu kafin ya garzaya da ita da jaririn zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Shi ma Shugaban Direbobin Adaidaita Sahu na yankin, Hussaini Sa’idu, ya ce matsalar hanyar ta ƙara tsananta wahalhalun da al’umma ke fuskanta, musamman mata masu juna biyu, yara da tsofaffi. Ya ce idan aka yi ruwan sama mai ƙarfi, ambaliya kan mamaye hanyar na sa’o’i, lamarin da ke katse zirga-zirga tare da hana jama’a isa kasuwanni, makarantu da cibiyoyin lafiya.

Advertisement

IMG 20260708 WA0003

Mazauna yankin sun roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sa baki domin tabbatar da komawar kamfanin da aka bai wa kwangilar zuwa bakin aiki ba tare da wani ƙarin jinkiri ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga hukumomin gwamnati ko kamfanin da ke gudanar da aikin kan dalilin jinkirin ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending