News
APC ta Tabbatar da Kashim Shettima A Matsayin Abokin Takarar Tinubu A Zaben 2027
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da sake zaɓar Mataimakinsa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa a zaɓen shekarar 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Advertisements
Advertisements
Jam’iyyar APC ce ta tabbatar da hakan a yayin wani biki da aka gudanar a yau Jumu’a, inda aka miƙa sunayen Shugaba Tinubu da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, ga Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, domin isar da su ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bisa tanadin dokokin zaɓe.
Advertisements
Advertisements
