Connect with us

News

Gwamnatin Tarrayya Ta Sanar Da Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Oyo

Published

on

741197055 10174698284055111 4605763959577579789 n (1)

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ceto ɗalibai da malamansu da aka sace a makarantu uku na jihar Oyo ta kudancin Najeriya, fiye da kwanaki 50 da yin garkuwa dasu yau.

Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaba Tinubu ne ya sanar da haka yau Jumma’a, inda ya ce jami’an tsaron ƙasar ne suka ceto su daga hannun ƴan ta’adda.

A ranar 15 ga watan Mayun da ya gabata ne, ƴan bindiga suka sace ɗalibai da malamai 46 cikin har da shugaban makaranta daga makarantun yankin Ogbomosho da ke jihar Oyo.

Kwanaki bayan harin, ƴan bindigar suka fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda suka yiwa wani malamin lissafi na guda cikin makarantun, Michael Oyedokun yankan rago, lamarin da ya haifar da zazzafar muhara.

Bayan hakan ne kuma, ƙungiyar malamai na NUT da sauran masu ruwa da tsaki suka gudanar da zanga-zanga don nunawa gwamnati fushinsu.

Haka zalika, matsin lamba ya gwamnati ya tsananta bayan fitar wani bidiyon Mrs Rachael Alamu, shugabar makarantar sakadire ta Ahoro-Esiele, inda ta ke roƙon mahukunta su gaggauta ceto su.

Advertisement

Sace ɗaliban dai ya ƙara janyowa gwamnatin Najeriya baƙin jini, kasancewar acan jihar Borno ma a rana guda aka sace wasu ɗalibai a Askira-Uba, abinda ya sake fito da irin yadda matsalar garkuwa da mutane ke neman zama ruwan dare a sassan ƙasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending