Connect with us

News

Mutum Ɗaya Ya Rasu, Huɗu Sun Jikkata Sakamakon Rushewar Gini a Kano

Published

on

IMG 20260710 141430 650

Mutum ɗaya ya rasu, yayin da wasu huɗu suka jikkata bayan wani gini ya rushe a titin Sultan da ke unguwar Nasarawa GRA a birnin Kano, ranar Juma’a.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Alhaji Isyaku Lawan Kubarachi, ya ce jami’an ceto tare da haɗin gwiwar al’umma sun ciro mutum biyar daga ƙarƙashin ginin da ya rushe.

BA MALAMI A MAAUN BANE: MAAUN Ta Nesanta Kanta Da Tsohon Malami Da Ake Zargi Da Kokarin Cin Zarafin Ɗaliba

Ya ce abin takaici, ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto ya rasu ne sakamakon munanan raunukan da ya samu, yayin da sauran huɗun ke ci gaba da karɓar kulawar likitoci.

Kubarachi ya buƙaci masu gine-gine da jama’a su riƙa bin ƙa’idojin aikin gini, tare da tabbatar da cewa ƙwararrun injiniyoyi ne ke kula da duk wani aikin gini domin kare rayuka da dukiyoyi daga irin waɗannan haɗurra.

Ya kuma isar da saƙon ta’aziyyar Gwamnatin Jihar Kano ga iyalan mamacin, tare da yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar Allah Ya ba su lafiya cikin gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending