Connect with us

News

Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku

Published

on

Atiku visits Obasanjo 1 1045x610 1 750x375

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, inda ya ce bai taɓa nadamar adawa da yunƙurin wa’adin mulki na uku ba, yana mai cewa ya fifita kare kundin tsarin mulkin Najeriya da dimokuraɗiyya fiye da biyayya ga mutum.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Asabar.

Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano 

Martanin ya biyo bayan kalaman Obasanjo na ranar Juma’a, inda ya ce zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa a zaɓen 1999 shi ne kuskuren siyasa mafi girma da ya taɓa yi.

Atiku ya ce kalaman Obasanjo wani yunƙuri ne na sake rubuta tarihin alaƙarsu ta siyasa da kuma gwamnatin da suka jagoranta na tsawon shekara takwas.

Ya ce ya kalli furucin tsohon shugaban ƙasar “cikin baƙin ciki, ba cikin fushi ba”, yana mai cewa tsohon shugaban ya bari ƙiyayya ta rinjayi gaskiyar tarihi.

Advertisement

“Na tsaya tsayin daka kan kundin tsarin mulki”

Atiku ya ce tushen saɓanin da ke tsakaninsu shi ne yadda ya ƙi goyon bayan yunƙurin gyaran kundin tsarin mulki domin bai wa Obasanjo damar yin wa’adi na uku.

“Ina alfahari da yadda na yi adawa da wa’adi na uku. Na tsaya kan kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya, kuma ba ni da wani nadama kan hana duk wani yunƙuri na tauye dimokuraɗiyya saboda son zuciya.”

Ya ƙara da cewa idan ƙiyayyar Obasanjo ta samo asali ne daga matsayinsa na ƙin amincewa da wa’adi na uku, to yana ɗaukar hakan a matsayin abin alfahari.

“Babu wani mutum da ya fi Najeriya girma. Kundin tsarin mulki shi ne mafi girma, kuma na zaɓi Najeriya da dimokuraɗiyya fiye da biyayya ga mutum.”

“Na taimaka wa Obasanjo lokacin da yake gidan yari”

Advertisement

Atiku ya kuma tuna da irin rawar da ya taka wajen tallafa wa Obasanjo lokacin da yake tsare a gidan yari a ƙarƙashin gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha.

Ya ce ya taimaka wa iyalansa, ya yi aiki tare da wasu domin ganin an sake shi, sannan bayan fitowarsa daga kurkuku ya ba shi cikakken goyon bayan siyasa da na rayuwa.

“Lokacin da aka sake shi, ba shi da komai sosai. Na karɓe shi, na tufatar da shi, na tabbatar an kula da shi, sannan na haɗa ƙawance da tsarin siyasa da suka taimaka wajen zama Shugaban Ƙasar Najeriya.”

Sai dai ya ce bai taɓa nadamar wannan taimako ba, domin kyautatawa ba ciniki ba ne.

Atiku ya kare rawar da ya taka a tattalin arziki

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ƙaryata duk wani yunƙuri na rage gudunmawar da ya bayar a gwamnatin Obasanjo.

Advertisement

Ya yi nuni da yabon da Darakta Janar ta WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta yi wa tawagar tattalin arzikin gwamnatin Obasanjo, yana mai cewa hakan shaida ce ta irin gudunmawar da ya bayar.

“A mai da hankali kan matsalolin Najeriya”

Atiku ya ce maimakon komawa kan tsoffin saɓanin siyasa, ya kamata shugabanni su mayar da hankali kan matsalolin da ke addabar Najeriya, kamar tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma farfaɗo da tattalin arziki.

Ya ce zaɓen 2027 ya kamata ya kasance kan yadda za a sake gina ƙasa da dawo da fata ga matasa, ba wai sake tayar da tsoffin rigingimun siyasa ba.

Asalin rikicin Atiku da Obasanjo

Obasanjo da Atiku sun yi mulki tare a matsayin Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa tsakanin 1999 zuwa 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Advertisement

Sai dai alaƙarsu ta lalace a wa’adi na biyu bayan Atiku ya yi adawa da yunƙurin wa’adi na uku ga Obasanjo. Daga baya Atiku ya fice daga PDP zuwa Action Congress inda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2007.

Rikicin ya kai har kotun ƙoli bayan Obasanjo ya ayyana kujerar mataimakin shugaban ƙasa a matsayin wadda babu kowa a kai bayan Atiku ya sauya jam’iyya. Sai dai Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa shugaban ƙasa ba shi da ikon tsige mataimakinsa wanda aka zaɓa ta hanyar zaɓe.

 

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending