Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano 

Published

on

IMG 20260801 WA0047

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta ƙwato na’urorin hasken rana (solar) guda 160 da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan 59.2, waɗanda ake zargin wani magidanci mai shekaru 43 ya sace tare da ɓoye su a wani kango da ke unguwar Haye, cikin yankin Sharaɗa.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa nasarar ta samu ne a wani samame da jami’an ’yan sanda suka gudanar bayan samun sahihan bayanan sirri, inda aka gano tare da ƙwato kayayyakin da ake zargin an sace.

INEC Ta Wallafa Bayanai: Tinubu Bai Cika Guraben Firamare Da Sakandare A Fom Din Takararsa Ba

Haka kuma, rundunar ta kama wasu magidanta uku da ake zargi da hannu a fashin famfon man fetur na wani gidan mai da ke Ƙaramar Hukumar Gaya. An kiyasta darajar kayayyakin da aka kwato daga hannunsu da kusan Naira miliyan 10.2.

A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun bayyana sun sayi kayan ne daga wani mutum ɗan asalin Jihar Kaduna. Sai dai mutumin ya tsere kafin jami’an tsaro su samu nasarar cafke shi, kuma ana ci gaba da farautarsa.

Rundunar ta tabbatar da cewa bincike kan lamarin na ci gaba, tare da alƙawarin kamo duk wani da ke da hannu a aikata laifin domin gurfanar da shi a gaban kotu.

Advertisement

 

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending