News
Ƴansanda Sun Cafke Mutane Takwas Kan Rikicin Kasuwar Gujungu Dake Jigawa
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta samu gagarumar nasara wajen yaƙi da manyan laifuka, bayan kama wasu da ake zargi da hannu a kisan kai, hare-hare kan jami’an tsaro da kuma rikicin da ya ɓarke a Kasuwar Gujungu da ke Ƙaramar Hukumar Taura.
Haka kuma, rundunar ta ce ta kwato shanu shida da ake zargin an bari a lokacin rikicin, yayin da take ci gaba da bincike kan lamarin.
Manufofin Gwamnatin Shugaba Tinubu Sun Jefa Yan Najeriya Cikin Matsin Rayuwa —Seyi Makinde
Mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
rundunar ta bayyana cewa rikicin Kasuwar Gujungu ya samo asali ne bayan wata sa-in-sa tsakanin wani soja da wani ɗan kasuwa mai suna Biniya Alhaji Ibrahim, mai shekaru 25 daga Ƙaramar Hukumar Miga, a ranar 26 ga Yuli.
Sanarwar ta ce ana zargin sojan da caka masa wuka, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsa.
Bayan faruwar lamarin, wasu fusatattun matasa sun kai hari ofishin ’yan sanda, tare da jefa wa jami’an tsaro kibiyoyi, sannan suka banka wa shaguna biyu wuta.
Rundunar ta ce bincike ya kai ga kama Muhammed Muhammed mai shekaru 22 daga Gagarawa da kuma Faridu Mohammed bisa zargin hannu a hare-haren, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda suka tsere.
