News
Gwamna Kano Abba Kabir Ya Samu Lambar Yabo Kan Ƙwarewa Wajen Gudanar Da Harkokin Tsaro
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu lambar yabo ta musamman kan ƙwarewa wajen gudanar da harkokin tsaro daga Cibiyar Nazarin Tsaro da Dabarun Tsaro (Institute of Security and Strategic Studies — ISSS).
An bai wa gwamnan lambar yabon ne bisa ƙoƙarin gwamnatinsa wajen ƙarfafa tsaro, kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tallafa wa hukumomin tsaro da kuma samar da matakan dakile laifuka da tabbatar da zaman lafiya a Kano da yankin Arewa maso Yamma.
Kano: Gini Ya Rufta Kan Dalibai A Makarantar Islamiyya
An gabatar da lambar yabon ne a taron Arewa maso Yamma kan Gudanar da Tsaron Al’umma da Dakile Laifuka da ISSS ta shirya a Jihar Kaduna, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, masana da sauran masu ruwa da tsaki.
ISSS ta ce ta gudanar da kima kan salon jagorancin Gwamna Yusuf da yadda gwamnatinsa ke tafiyar da harkokin tsaro, musamman wajen kare jama’a, tallafa wa hukumomin tsaro, hulɗa da al’umma da haɗa kan hukumomi wajen tinkarar barazanar tsaro.
Gwamnan ya samu wakilcin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda ya bayyana lambar yabon a matsayin babbar girmamawa da kuma ƙarin ƙwarin gwiwa ga gwamnatin Kano.
Waiya ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, shugabannin al’umma da ƙungiyoyin farar hula domin inganta tsaro, yana mai cewa haɗin kan al’umma na da muhimmiyar rawa wajen samar da bayanan sirri da gano barazana tun da wuri.
A nasa jawabin, Dr Muhammad Ali ya yi kira da a ƙara ƙarfafa tsarin tsaro da ya shafi al’umma, musayar bayanan sirri da tsarin gargaɗin farko, domin gano matsalolin tsaro da wuri tare da mayar da martani cikin gaggawa. Taron ya kuma ƙare da kira ga duk masu ruwa da tsaki da su ƙara haɗin gwiwa wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Arewa maso Yamma.
