News
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya shigar da ƙara a kan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), inda ya nemi kotu ta ba shi diyyar Naira biliyan 10 kan zargin hana shi ganawa da wasu daga cikin iyalansa.
El-Rufa’i ya shigar da ƙarar ne a ranar Lahadi, inda ya zargi hukumar da hana matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufa’i, ganawa da shi yayin da yake tsare.
Akwai Yiwuwar Ballewar Dam Ɗin Challawa — Gwamnatin Tarayya
Lauyan tsohon gwamnan, Ubong Akpan, ne ya shigar da ƙarar, wadda ke ɗauke da lamba FHC/ABJ/CS/1852/2026. A cikin ƙarar, an sanya Shugaban ICPC da Antoni Janar na Tarayya (AGF) a matsayin waɗanda ake ƙara na biyu da na uku.
A ƙarar, El-Rufa’i ya nemi kotu ta amince da wasu buƙatu guda tara, ciki har da ayyana cewa haƙƙoƙin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya ba shi suna ci gaba da aiki, duk da kasancewarsa a tsare.
Ya kuma nemi kotun ta ayyana cewa hana iyalansa ziyartar sa, musamman domin kai masa abinci, kula da lafiyarsa da sauran buƙatunsa, ba tare da ingantaccen umarnin doka ba, ya zama tauye masa haƙƙin ɗan Adam.
Tsohon gwamnan ya kafa hujja da tanade-tanaden Sashe na 34 da 37 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, da kuma Sashe na 5 da 18 na Yarjejeniyar Afirka kan Haƙƙin Ɗan Adam da Jama’a.
Haka kuma, El-Rufa’i ya zargi jami’an ICPC da hana matarsa da ɗansa ganawa da shi, tare da zargin cewa jami’an sun wulaƙanta su a ranar 7 ga Yuli. Ya ce hakan ya shafi haƙƙinsa na mutunci da rayuwar sirri da kuma alaƙar iyali.
Daga ƙarshe, tsohon gwamnan ya roƙi kotun da ta umarci waɗanda ake ƙara da su ba shi damar ganawa da iyalansa yayin da yake tsare, yana mai cewa hakan ya yi daidai da wani umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar a baya.
