News
Mutane Huɗu Sun Mutu Bayan Cin Amala A Kogi
Mutane huɗu yan gida ɗaya sun mutu a garin Ihima da ke Ƙaramar Hukumar Okehi ta Jihar Kogi, bayan sun ci Amala.
Lamarin ya faru ne a Ihima, inda rahotanni suka ce karen gidan ma ya mutu bayan cin Amala.
’Yan Bindiga Sun Sace Mutune 60 Ana Tsaka Da Salla A Masallaci A Neja
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da cewa Amala ce ta haddasa mutuwar mutanen ba, yayin da gwamnatin jihar ta ƙaddamar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya umarci Kwamishinan Lafiya da ya fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya ce binciken zai mayar da hankali kan yiwuwar gurɓacewar abinci ko gubar abinci, da kuma wasu dalilai na lafiya ko muhalli da ka iya haifar da mutuwar.
Fanwo ya ce za a binciki samfurori da sauran shaidu da ke akwai domin gano gaskiyar abin da ya faru, kamar yadda ka’idojin lafiyar jama’a suka tanada.
Ya ƙara da cewa rahoton mutuwar karen gidan bayan cin abincin zai kasance cikin abubuwan da binciken zai duba.
Kwamishinan ya ce Ma’aikatar Lafiya za ta yi aiki tare da sauran hukumomi da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa binciken ya kasance cikakke, tare da ɗaukar matakan da suka dace idan aka gano musabbabin lamarin.
Gwamnatin jihar ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da kauce wa yaɗa jita-jita ko yin hasashe kan musabbabin mutuwar har sai an kammala binciken.
Gwamna Ododo ya jajanta wa iyalan mamatan da al’ummar Ihima bisa wannan mummunan lamari, yana mai addu’ar Allah Ya ba su haƙurin jure wannan rashi.
-
Uncategorized3 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News6 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
-
News2 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
