Connect with us

News

Gwamnatin Kano Za Ta Tallafa Wa Duk Wani Yunkurin Da Zai Kawar Da Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ce a shirye take ta tallafa wa duk wani yunƙuri da zai taimaka wajen kawar da matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da gidauniyar The Recovery Hub, wadda aka kafa domin tallafa wa mutanen da ke fama da matsalar shaye-shaye da kuma wayar da kan al’umma kan illolin amfani da miyagun ƙwayoyi.

Ba Za A Gudanar Da Zaɓen Gwamna A Jihohi 8 Ba

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ɗaukar matsalar shaye-shaye da matuƙar muhimmanci, saboda illolin da take haifarwa ga lafiyar al’umma, musamman matasa.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shirye da ƙungiyoyin da suke da manufar yaƙi da shaye-shaye, tare da haɗa kai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile matsalar.

“Gwamnati a shirye take ta taimaka wa duk wani yunƙuri da zai taimaka wajen kawar da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi,” in ji shi.

Advertisement

Ya jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro, ƙwararrun ma’aikatan lafiya, ƙungiyoyin fararen hula da al’umma na da muhimmiyar rawa wajen samun nasara a yaƙi da matsalar.

Da yake jawabi, Shugaban Gidauniyar The Recovery Hub, Dr Abdullahi Akilu, wanda likitan ƙwaƙwalwa ne a Asibitin Dawanau da ke Kano, ya nuna damuwa kan yadda matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke ƙara yaɗuwa a tsakanin al’umma.

Dr Akilu ya ce an kafa gidauniyar ne domin wayar da kan jama’a kan illolin shaye-shaye, da kuma samar da tallafi da kulawa ga mutanen da ke fama da matsalar.

Ya ƙara da cewa gidauniyar za ta taimaka wa waɗanda suka samu sauƙi daga matsalar shaye-shaye wajen farfaɗowa da sake komawa cikin al’umma.

A cewarsa, matsalar miyagun ƙwayoyi ta zama babbar barazana ga al’umma, lamarin da ya ce ya sa ake buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, hukumomin tsaro, ma’aikatan lafiya da sauran masu ruwa da tsaki domin magance ta.

Shi ma Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwar Hukumomin Jihar Kano kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Fataucin Haramtattun Abubuwa, Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce kwamitin zai haɗa kai da The Recovery Hub domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar.

Advertisement

Muhuyi ya ce haɗin gwiwar hukumomi da ƙungiyoyin da ke tallafa wa masu fama da shaye-shaye na da muhimmiyar rawa wajen rage matsalar da kuma kare matasa daga faɗawa cikin tarkon miyagun ƙwayoyi.

Ya yi kira ga iyaye, malamai da shugabannin al’umma da su ƙara ƙoƙari wajen wayar da kan matasa kan illolin shaye-shaye, tare da kulawa da halayensu domin taimaka musu guje wa faɗawa cikin matsalar.

Taron ƙaddamar da gidauniyar ya samu halartar wakilan hukumomin tsaro, ƙungiyoyin lafiya, likitoci da sauran masu ruwa da tsaki.

Daga cikin mahalarta akwai wakilan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, manyan likitoci daga Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, wakilan Asibitin Dawanau da kuma Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA).

Haka kuma, wakilan ƙungiyoyin fararen hula, ciki har da Youth Awareness Against Drug Abuse Initiative, da ’yan jarida sun halarci taron.

An jaddada muhimmancin haɗin gwiwar hukumomi da ƙungiyoyi wajen yaƙi da matsalar shaye-shaye, da wayar da kan al’umma, musamman matasa, tare da samar da kulawa da tallafi ga masu fama da matsalar domin taimaka musu wajen farfaɗowa da sake komawa cikin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending