Connect with us

News

NEJA:Sabuwar Zanga-zanga Ta Barke Kan Rashin Tsaro

Published

on

41399f06 62df 4643 a46c 6b7115064ce5

Al’ummomin ƙananan hukumomin Borgu da Agwara a Jihar Neja sun tare hanyar Mokwa zuwa New Bussa, yayin da suke zanga-zangar nuna rashin amincewa da yadda hare-haren ’yan bindiga ke ƙaruwa a yankin.

Masu zanga-zangar, waɗanda suka haɗa da matasan Borgu da ’yan kungiyar NURTW, sun fara tare hanyar tun misalin 5:30 na safe a shataletalen Bussa.

Sama Da Yankuna 8,000 Da Makarantu 4,500 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa    — Gwamnatin Tarayya 

Sun ce zanga-zangar ta biyo bayan kalaman Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, cewa mutum 30 ne aka yi garkuwa da su a hare-haren da aka kai wasu masallatai a yankin Dekara da sauran al’ummomi.

Sai dai Mai Binciken Kuɗi na Gamayyar Matasan Borgu, Aliyu Abdulmajeed, ya ce kusan mutane 500 ne har yanzu suke hannun ’yan bindiga, bayan an sace su makonni uku da suka gabata.

Ya kuma yi zargin cewa an kashe wasu daga cikin waɗanda aka sace, ciki har da mutane 30 da aka ce an gano gawarwakinsu bayan an sare kawunansu.

Advertisement

Abdulmajeed ya ce hare-haren sun kuma janyo rikicin ƙabilanci tsakanin manoma da makiyaya a Agwara, inda ya ce mutane takwas sun mutu cikin makonni biyu, yayin da daruruwa suka rasa gidajensu.

Ya ƙara da cewa harin da aka kai yankin Guchana na Borgu a ƙarshen mako ya raunata kusan ’yan sa-kai 30, waɗanda a cewarsa ba su samu damar zuwa asibiti ba.

A nasa bangaren, Shugaban Ƙaramar Hukumar Borgu, Mohammed Nasir Abdullahi, ya ce an tura jami’an tsaro yankin domin dakile hare-haren, bayan gwamnatin jihar ta nemi taimakon Gwamnatin Tarayya.

Ya ce hare-haren da aka kai masallatan Juma’a a Dekara, Gbezhin, Sabon-Gida da Kpenya a ranar 21 ga Agusta sun yi sanadin sace masu ibada da dama, daga bisani aka kashe kusan 30 daga cikinsu.

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma ce babu wani sabon hari da aka samu tun bayan waɗannan hare-hare, yana mai cewa bidiyon da ke yawo a baya-bayan nan game da sabbin hare-hare ba gaskiya ba ne.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending