News
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Biyu Bisa Zargin Mallakar Bindigu Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu bisa zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Laraba.
Kaduna: Ma’auratan Da Aka Sace Tare Da Jaririyarsu Sun Kuɓuta
A cewar sanarwar, jami’an sa ido na rundunar da ke Cibiyar Farm Centre sun kama waɗanda ake zargin ne yayin da suke gudanar da sintiri a kan titin Sakkwato Road.
Sanarwar ta ce jami’an sun tsayar da wani babur mai ƙafa uku, wato Keke Napep, domin gudanar da bincike, inda suka gano bindiga a cikin jakar wani mutum mai suna Rufa’i, mazaunin unguwar Hotoro, tare da harsasai.
Haka kuma, jami’an sun kama Aliyu Ibrahim, mai shekaru 19, mazaunin unguwar Kawo, bisa zargin kasancewa da hannu a harkar mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Rundunar ’yan sandan ba ta bayyana ƙarin bayani kan irin makaman da aka samu hannun wanda ake zargin na biyu ba a cikin bayanan da aka bayar..
