Connect with us

News

Gwamnatin Tarrayya Ta Kama Wasu Da Ake Zargi Da Aikin Rajistar Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa  NIN Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Published

on

3b530d99 12a8 46fc bd4f c5b05571f410 1793637502509
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa ta Nijeriya (NIMC) ta kama wasu mutane da ake zargi da gudanar da rajistar lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) ba bisa ƙa’ida ba a Gwagwalada da ke birnin Abuja da wasu wurare, a wani mataki na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rajistar da ba ta da izini, sauya bayanan mutane ba bisa ƙa’ida ba da kuma karɓar kuɗi ta hanyar cuta.

A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labaran hukumar, Kayode Adegoke, ya fitar, NIMC ta ce sashen sa ido kan bin ƙa’ida da aiwatar da doka na hukumar ya kuma ƙwace wasu na’urori da ake zargin waɗanda aka kama suna amfani da su wajen gudanar da ayyukan.

Gwamnatin Kano Ta Kama ’Yan Kasuwa Kan Sauya Wa Madarar Gari Wa’adin Ƙarewa

Babbar daraktar hukumar, Abisoye Coker-Odusote, ta sake jaddada cewa NIMC ba za ta lamunci karɓar kuɗi ta hanyar cuta ko wasu munanan halaye da suka saɓa wa ƙa’idojin aiki ba.

Hukumar ta kuma jaddada cewa dole ne a gudanar da rajistar NIN a cibiyoyin da gwamnati ta amince da su kawai, yayin da duk wata buƙatar sauya bayanan mutum dole ne a bi ta hanyar da hukumar ta amince da ita ta intanet wadda mutum zai iya yi da kansa.

Haka kuma, hukumar ta buƙaci masu lambar NIN da su riƙa amfani da hanyoyin da aka amince da su kawai wajen biyan buƙatunsu da suka shafi NIN, tare da sauke manhajar NINAuth, wadda ke samar da ƙarin matakan tsaro, ciki har da kare lambar NIN da kuma damar buga takardar shaidar NIN.

Advertisement

Wannan kamen na daga cikin ƙoƙarin hukumar na ƙarfafa tsaron kundin bayanan shaidar ‘yan Nijeriya da kuma kare jama’a daga ayyukan damfara, rajistar da ba ta dace ba da kuma amfani da bayanan sirrinsu ba tare da izini ba.

 

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending